Isra'ila da Hamas sun cimma tsagaita wuta a Gaza
January 15, 2025Talla
Jami'an Qatar da na Hamas sun ce sun cimma matsaya na tsagaita wuta a fadan da ake yi tsakanin Hamas da Israila
Firaministan Qatar Mohammed ben Abdelrahmane Al-Thani wanda ke shiga tsakani a tattaunawar, ya gana da tawagogin Hamas da na Isra'ila dabam-daban a birnin Doha
jim kadan bayan ganawar firaministan ya ce an warware y'ar takaddama da ta so hanna ruwa guda a tattaunawar, amma yanzu ya ce an samu daidaituwar baki
Yarjejeniyar dai ta tanadi dakatar da bude wuta nan take, tare da sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza