1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Hamas sun gaza cimma daidaito kan yakin Gaza

April 8, 2024

Jami'an Isra'ila da na Hamas sun watse baram-baram daga tattaunawar sulhu da ake gudanarwa a Masar tare da kawo karshen fatan da aka dade ana yi kan yuwuwar sakin fursunoni da kuma tsagaita wuta a zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4eYAX
Gazastreifen | Zerstörungen in Khan Yunis
Hoto: AFP/Getty Images

Tun da farko dai wani kamfanin dillancin labaran gwamnatin Masar ta ruwaito cewa ana samu gagarumin ci gaba a tattaunarwar da bangarorin biyu ke yi, bayan share tsawon watanni shida ana barin wuta tsakanin dakarun Isra'ila da kungiyar Hamsa a dan karamin yankin na Falasdinu.

Karin bayani: Blinken na matsa wa Isra'ila lamba don tsagaita wuta a Gaza

A daya gufe kuma duk da matsin lambar da take sha daga kasashen duniya, Isra'ila ta kekasa kai kasa kan shirinta na kutsawa Rafha ta kasa, birni daya tilo da a halin yanzu ya ragewa al'ummar Falasdinu inda mutum miliyan guda da rabi ke a tsugune.

Hasali ma firaministan Isra'ilar Benjamin Netenyahu ya jadada cewa dakarun kasar na shirye-shiyen kutsawa birnin da ke iyaka da Masar wanda ya bayyana a matsayin tungar mayakan kungiyar Hamas wace ya sha alwashin yaka ba gudu ba ja da baya.

Karin bayani: Sojojin Isra'ila sun fara ficewa daga Zirin Gaza

Tuni ma wannan ikirari ya tsoratar da Falasdinawa tare da sa su fara ficewa daga Rafah, lamarin da ya kai da dama yin takattaki zuwa  birnin Khan Younes inda kura ta fara lafawa bayan kwarya-kwaryan janyewar dakarun Isra'ila.