1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaGabas ta Tsakiya

Isra'ila da Iran: Wace ce ta fi karfin soji?

Kersten Knipp ZMA
April 22, 2024

Tun bayan da Isra'ila ta ayyana yin martani kan harin da Iran ta kai da jirage marasa matuka, kasashen duniya suka shiga kira ga bangarorin biyu kan bukatar su kai zuciya nesa.

https://p.dw.com/p/4f4Gm
Hoto: Vahid Salemi/AP/picture alliance

Duba da cewar hakan zai iya fadada rikici a yankin Gabas ta Tsakiya da tuni ke cikin wadi-na-tsaka-mai wuya. Amma ko shin Isra'ila da shirya tinkarar wannan rikici?

A bayyane yake cewa dole ne Isra'ila ta yi la'akari da abubuwan da ke da wuyar kididdigewa, ciki har da tambayar ko kawayen Iran da ba na gwamnati ba za su shiga cikin rikicin. Babban abokiyar kawancen ita ce kungiyar Hizbullah da ke samun tallafin Iran a Lebanon. Mayakan Houthina Yemen, daura da wasu mayakan Shi'a a Iraki wadanda su ma za su iya shiga cikin wannnan rikici na makami ko kuma Iran ta dauke su a matsayin masu goyon bayan soji.

Israel Tel Aviv Sitzung Kriegskabinett
Majalisar kula da yaki ta Isra'ilaHoto: Israeli Government Press Office/Anadolu/picture alliance

Daya daga cikin kakakin rundunar sojin Is'raila Arye Sharuz Shalicar ya ce Isra'ila ta dade tana shirin fuskantar hadarin irin wannan yaki, inda aka fi mayar da hankali kan wasu mihinmman abubuwa guda uku.

"Na farko shi ne, ko shakka babu mun fadadatsarin tsaron mu. Ina tsammanin kun san yawancinsuna kare makamai masu linzami na ballistic, muna da tsarin tsaro mai yawa a nan. Kuma wannan shi ne abu daya da muka fadada sosai. Abu na biyu shi ne kwarewarmu, wanda ke nufin yadda muke kawar da jirage marasa matuka masu shigowa ta sararin samaniya, misali, ta hanyar tunkarar su da jiragen yaki. Na uku kuwa, shi ne hadakar kasashe kawayenmu da ke wannan yankin da wasu yankuna, kamar yadda ya kasance a daren  daren Asabar zuwa Lahadi, lokacin da Iran ta kawo mana hari".

Iran Teheran | Iranische Soldaten
Sojojin IranHoto: Vahid Salemi/AP/dpa/picture alliance

Bisa ga kididdgar cibiyar nazarin karfin soji ta Global Firepower na wannan shekara ta 2024 dai, a fuskar karfin soja gaba daya, sojojin Isra'ila da na Iran ba su da nisa sosai. Iran ce ta 14 a jerin kasashen duniya da suka fi karfin soji, a yayin da Isra'ila ke a matsayi na 17. Bugu da kari cibiyar ta kuma kwatanta yawan sojojin bangarorin biyu kai tsaye. Wanda ya nunar da cewar, Iran ta fi Isra'ila fifiko wajen yawan runduna mai karfi, kazalika haka yale a bangaren abun da ya shafi adadin tankokin yaki da motoci masu dauke da makamai.

Duk da haka, wannan ba shi da mahimmanci idan aka yi la'akari da yanayin yankin. Isra'ila da Iran dai na da wasu kasashe kamar Iraki da Jordan a tsakaninsu, kuma akwai tazarar kusan kilomita 1,850 da ke tsakanin Kudus da Tehran. Fabian Hinz, kwararre ne a kan Gabas ta Tsakiya a Cibiyar Nazarin Dabaru ta Duniya da ke London.

Iran ballistische Rakete / Israel / Nahostkonflikt
Hoto: Itamar Grinberg/AP Photo/picture alliance

"A hakikanin gaskiya, wannan rikici ba zai zama wani salo na yaki ba, sai dai wani nau'i ne na musanyar bugu daga dogon zango. Amma kuma yaki a bangare guda ta karkashin Hizbullah a Lebanon, na iya zama kamar yaki na zahiri a dabarbarce."

A cewar wata kididdiga ta Global Firepower, a bayyane yake cewa Isra'ila ta fi Iran a bangaren jiragen yaki ta sama. A yayin da Isra'ilake da jiragen yaki 241, Iran a daya hannu na da 181. A jimilce sojojin Isra'ila na da jiragen sama 612, yayin da Iran ke da 551.