1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila na ci gaba da kai hari a kan Hamas

Mouhamadou Awal Balarabe
May 11, 2021

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen kai hare-hare a kan Hamas, bayan ruwan rokoki da kungiyar ta yi a kudancin kasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

https://p.dw.com/p/3tGOg
Gaza Luftangriff Israel
Hoto: Hatem Moussa/AP Photo/picture alliance

Luguden wuta da Isra'ila ta yi a Zirin Gaza a matsayin martani ya jawo asarar rayukan akalla Falasdinawa 28. Tuni ma sojojin Isra'ila suka lalata bene mai hawa goma a lokacin da suka kai wa Hamas hari a Zirin Gaza don daukar fansa.

Sai dai reshen kungiyar Hamas da ke dauke da makamai na ci gaba da yi wa Isra'ila barazanar fadada hare-hare idan dakarunta ba su janye daga masallacin Kudus ba. Sannan tana lasar lasar takobin ragargaza garin Ashkelon, idan hare-haren Isra’ila suka jikkata wasu karin fararen hula a Gaza. 

Ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz ya amince da bukatar da sojojin suka gabatar na neman karin dakaru 5,000 don tinkarar Falasdinawa. Amma ba a bayyana lokacin da za a aiwatar da wannan shawarar ba.