Isra'ila na shan suka kan farmakin da ta kai Rafah
February 15, 2024Bayan Amurka da ke zama babbar kawar Isra'ila da ta ce ba ta goyon bayan farmakin, kasashen Kanada da Ostraliya da kuma New Zealand sun bi sahu inda a wannan Alhamis suka gargadi gwamnatin Netanyahu na ta gaggauta dakatar da kutsen da sojojinta suka fara yi a yankin.
Karin bayani: MDD ta bukaci da a dakatar da Isra'ila daga kai hari a Rafah
Kasashen uku na Commonwealth sun nanata cewa babu wani matsuguni da ya rage wa Falasdinawa kusan miliyan 1,5 da suka makale a birnin na Rafah da ke kan iyaka da Masar, suna masu kira ga Benjamin Natenyahu da kadda ya aiwatar da wannan mummunan mataki.
Karin bayani:Mace-mace na karuwa a Rafah saboda luguden wuta na Isra'ila
A safiyar Alhamis 15.02.2024 ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayar da rahoton cewa dakarun na Isra'ila sun halaka mutane 107 galibi mata da yara a jerin hare-haren da suka kai a daren ranar, sannan kuma sun halaka mutum guda tare da jikkatar da wadansu a wani asibiti da ke Khan Yunus a kudancin Gaza.