Isra'ila ta ce ta kammala harin ramuwar gayya kan Iran
October 28, 2024Rundunar sojin Israila ta kai harin ramuwar gayya kan cibiyoyin soji a kasar Iran a farmakin da ta shafe sa'oi hudu da sanyin safiyar wannan Asabar din.
Sai dai sojojin Isra'ilar sun ce sun kammala harin na ramuwar gayya. Ta kuma gargadi Iran kan sake mayar da matani.
Amma kuma Iran din ta ce za ta mayar da martani, sai dai ba ta baiyana yanayi da kuma lokacin da za ta mayar da martanin ba.
Hare haren sojin Isra'ilar na matsayin ramuwa ga hare haren da Iran ta kai wa Isra'ila a ranar 1 ga watan Oktoba inda ta harba mata makamai masu linzami kusan 200
Hare haren na Iran sun biyo bayan kisan shugaban Hizbullah Hassan Nasrallah a karshen watan Satumba a Lebanon da kuma kisan jagoran Hamas Ismaila Haniyeh wanda ya rasu a wani harin bam a Tehran a cikin watan Yuli wanda Iran ta dora alhakin kisan sa a kan Israila.