1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta gargadi kasar Iran

February 18, 2018

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gargadin kasar Iran da ta guji duk wani yunkuri na tunzura Isra'ila, bayan tabbatar da harbe jirgin Iran mara matuki a cikin kasarsa a makon jiya.

https://p.dw.com/p/2stYq
München MSC 2018 | israelischer Ministerpräsident Benjamin Netanjahu
Firaministan Isra'ila, Benjamin NetanyahuHoto: picture-alliance/dpa/MSC 2018/L. Preiss

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gargadin kasar Iran da ta guji duk wani yunkuri na tunzura Isra'ila, bayan tabbatar da harbe jirgin Iran mara matuki a cikin kasarsa a makon jiya. Mr Netanyahu wanda ya nuna wani tarkacen da ya ce na jirgin Iran din da aka kakkabe a sararin kasar tasa ne, ya ce muddin aka kyale iran ta mallaki makamashin nukiliya, to fa babu wanda zai isa ya ja mata birki.

Firaministan na Isra'ila da ke magana a karshen taro kan al'amuran tsaro na birnin Munich dake nan Jamus, ya ce koda yake take-taken Iran din ga Isra'ila wata aba ce babba, a daya hannun ya inganta dangantakar kasar da wasu kasashen larabawa.

Ya kuma zargi ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif, wanda ya wakilci kasar a taron na birnin Munich da iya sharara karya kan cewar Iran din ta ki amincewa da aika jirginmarar matuki.