1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta halaka akalla mutum 50 a zirin Gaza

January 3, 2025

Jiragen saman kasar sun rika luguden wuta a wurare daban-daban ciki har da sansanin da aka ware a matsayin tudun tsira.

https://p.dw.com/p/4omQu
Daya daga cikin wurare da Isra'ila ta ragargaza a yakinta na Gaza shi ne Jabaliya.
Daya daga cikin wurare da Isra'ila ta ragargaza a yakinta na Gaza shi ne Jabaliya.Hoto: Mohammed Alaswad/AP

Luguden wuta da Isra'ila ta yi a tsakiya da kuma Kudancin zirin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mutum akalla 50.

Daya daga cikin wuraren da jiragenta suka yi ruwan wuta har da wani sansanin jinkai da aka kebe a matsayin tudun mun tsira domin bada agaji.

Isra'ila ta kashe likitoci da dan jarida a Gaza

Kamar yadda ta saba fadi, Isra'ila ta ce farmakin ya hari wani babban jam'in dansanda ne kuma ta zargi Hamas da mutuwar fararen hula.

Tun a ranar Alhamis sojojin na Isra'ila suka fara ruwan wutan da ya halaka adadin wadannan mutanen har zuwa yau Juma'a sannan akwai yara kananan da suka rasu sakamakon hare-haren.

Shugaban WHO ya tsallake rijiya da baya a harin Isra'ila

Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya ce ya umurci wata tawaga daga kasarsa ta ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta da ake yi a kasar Qatar.