1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta halaka wani jaroran Hezbollah a Siriya

Gazali Abdou TasawaDecember 20, 2015

Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da mutuwar jagoranta a Siriya Samir Kantar a lokacin wani harin da jiragen yakin sojin Isra'ila suka kaddamar a birnin Jaramana na kusa da birnin Damas na kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/1HQjK
Libanon Samir Kuntar ehemaliger PLF-Anführer
Hoto: Getty Images/H. Prison

Kungiyar Hezbollah ta tabbatar da mutuwar wani jagoranta a Siriya Samir Kuntar a lokacin wani harin da jiragen yakin sojin Isra'ila suka kaddamar a birnin Jaramana na kusa da birnin Damas na kasar Siriya.Kungiyar 'yan Shi'ar kasar ta Labanan ta tabbatar da wannan labari ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Lahadi.

A Shekara ta 2008 ne kasar Isra'ila ta sako Samir Kantar daga kaso a karkashin wata masayar firsuna da kuma gawarwaki da aka yi tsakanin Kungiyar Hezbollah da Isra'ilar wacce ke tsare da Kantar din tun a shekara ta 1980 bayan da kashe wasu Isra'ilawa uku da suka hada da dan sanda .Ana bayana Samir Kuntar a matsayin jagoran kungiyar 'yan Siriya masu fafutkar kwato yankin Golan daga hannun Isra'ila.