1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai farmaki gabar yamma

Abdullahi Tanko Bala
January 21, 2025

Rundunar sojin Israila ta ce jami'anta sun fara wani farmakin yaki da ta'addanci a birnin Jenin da ke yankin gabar yamma da kogin Jordan 'yan kwanaki bayan yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin Falasdinawa na Gaza.

https://p.dw.com/p/4pRff
Jami'an tsaron Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin
Jami'an tsaron Falasdinawa a sansanin 'yan gudun hijira na JeninHoto: Jaafar Ashtiyeh/AFP

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ce akalla mutane biyu sun rasa rayukansu wasu kuma sun sami raunuka a harin da Israila ta kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira.

Haka ma dai wani harin da Israila ta kai kan sansanin 'yan gudun hijira a makon da ya gabata ya hallaka akalla mutum uku.

Farmakin ya biyo bayan makonni da jami'an tsaron hukumar gudanarwar Falasdinawa suka yi ne na karbe iko da sansanin 'yan gudun hijirar na Jenin wanda ya kasance tungar kungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai.