1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari kan barikin sojoji a Siriya

Gazali Abdou Tasawa
September 7, 2017

Jiragen yaki Isra'ila sun kaddamar da wasu jerin hare-hare da safiyar wannan Alhamis kan wata cibiyar sojojin Siriya da ke a Yammacin kasar inda mutane biyu suka halaka. 

https://p.dw.com/p/2jWZQ
Israel Kampfjet der Luftwaffe
Hoto: Getty Images/AFP/J. Guez

A cikin wata sanarwa da ta fitar rundunar sojojin kasar ta Siriya ta tabbatar da afkuwar lamarin inda ta ce da misalin karfe biyu da mintoci 42 na dare ne jiragen yakin kasar ta Isra'ila suka harbo makamai masu linzami tun daga sarararin samaniyar kasar Lebanon zuwa kan cibiyar dakaranta da ke kusa da birnin Mesyaf , kuma harin ya lalata kadarori da halaka mutane biyu. 

Isra'ila dai na zargin wannan barikin sojoji ta gwamnatin Siriyar da ke kunshe da  wata cibiyar binciken kimiyya ta kasar da ake kira SSRC da kera makamai masu guba. Amma kuma rundunar sojin gwamnatin Siriyar ta kuma yi kashedi dangane da wannan hari da Isra'ila ta kai mata da ta ce na iya yin munmunan tasiri ga zaman lafiyar yankin baki daya.