1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari kan mabuyar Hamas daga Isra'ila

Abdoulaye Mamane Amadou
August 14, 2020

Rundunar sojan Isra'ila ta yi luguden wuta kan wasu wuraren da ta kira maboyar baraden kungiyar Hamas a Zirin Gaza, a wani yunkuri na takaita hare-haren daga yankin.

https://p.dw.com/p/3gwhf
Bildkombi Fahne von Israel und Fahne der Vereinigten Arabischen Emirate

Farmakin na Isra'ila na zuwa ne 'yan sa'o'i kalilan bayan bayyana cimma wata yarjejeniyar kyautata huldar diplomasiya tsakanin Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa a wani yunkuri na kama hanyar tabbatar da zaman lafiyar yankin, yarjejeniyar da hukumomin Filasdinu da kungiyar Hamas mai iko da Zirin Gaza suka yi fatali da ita.

Tuni kasashen duniya da dama ke ci gaba da yin tsokaci kan yarjejeniyar tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra'ila, kasa ta baya bayan nan ita ce Iran wadda ta kwatanta yarjejeniyar a matsayin mai cike da hadari, kana wata yaudara ga batun zaman lafiyar yankin.