Isra'ila: Watsi da sauya dokar zama dan kasa
July 6, 2021Talla
Majalisar dokokin Isra'ila a wannan Talatar ta kada kuri'ar kin amincewa da sauya dokar nan mai cike da sarkakkiya da ta hana bayar da shedar zama dan kasa ga Palasdinwan da ke yanki zirin Gaza masu auren Yahudawa ko kuma yan asalin kasar.
Batun hakan na zama wani tarnaki na farko da gwamnatin hada ka kalkashin jagorancin sabon firaministan kasar Naftali Bennett ta fara cin karo da shi. Majalisar ta Knesset ta gaza cimma wannan kudurin na sauya ayar dokar ta shekara ta 2003.
Dubun-dubatar iyallai ne dai wannan dokar ke yin mummunan tasiri a kansu shekara da shekaru.