1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Tsagaita wuta a Zirin Gaza

August 7, 2022

A kokarinta na shiga tsakani, kasar Masar ta ce Isra'ila ta amince da bukatarta ta sasantawa da Falasdinawan da ke zirin Gaza, bayan kwashe tsawon kwanaki ana gwabza fada.

https://p.dw.com/p/4FEi4
Palästinenser suchen in den Trümmern eines Wohnhauses
Hoto: Ismael Mohamad/UPI/IMAGO

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinawa ta ce ana cigaba da tattauna kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Wata majiya daga bangaren Masar ta ce Isra'ila ta amince ta tsagaita wuta, sai dai gwamnatin Cairo na jiran martanin Falasdinawa. Ana dai fatan yunkurin na Masar ya kawo karshen mummunan rikicin da aka ga irinsa na tsawon kwanaki 11 a shekarar bara.

Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ce  dai Isra'ila ta fara kai hare-hare ta sama kan maboyar 'yan kungiyar Islamic Jihad a Zirin Gaza, inda mayakan suka harba daruruwan rokoki a matsayin ramuwar gayya. Alkalumma na nuni da cewa kimanin Falasdinawa 31 ne suka rasa rayukansu ciki har da yara 6 yayin da wasu fiye da 250 suka jikkata.