1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: ISWAP ta dauki alhakin hari

Salissou Boukari LMJ
January 15, 2020

Kungiyar ISWAP ta masu ikirarin kishin adinin Islama a yankin yammacin Afirka, ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Nijar 89 a barakin sojoji na Chinagodrar.

https://p.dw.com/p/3WEcq
Frankreich G5-Sahel Gipfel in Pau
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: DW/F. Tiassou

Sai dai kungiyar ta ISWAP ba ta sanar da adadin mayakanta da sojojin na Nijar suka kashe ba. Kungiyar ta kuma wallafa hotunan gawarwakin sojoji da motoci da ta ce ta kwace su ne daga sojojin. Kungiya ta ISWAP dai na kiran kanta da kungiyar IS a yankin yammacin Afirka, ta kai wannan harin a Chinagodrar da ke kan iyakar Nijar da Mali ne, kimanin wata guda bayan wanda ta kai a barakin sojoji na Inates da shi ma ke da iyaka da kasar ta Mali. Bincike dai ya nunar cewa 'yan wannan kungiya sun samu gindin zama ne a wani yanki na kasar Malin, inda babu alamar gwamnatin ta Mali suke kuma cin karansu babu babbaka, abun da ke ba su damar samun tattara mutanensu daruruwa domin su kai harin inda suke so kan jami'an tsaro. Alkassoume Abdourahamane wani mai sharhi ne kan harkokin tsaro a Afirka ya kuma ce babu wani abin mamaki kan daukar nauyin harin da kungiyar ta ISWAP ta yi.

Kungiyar ta addabi kasashen Sahel

Ita dai wannan kungiyar da Adnane Abou Walid Al-Sahraoui ya kafa a yankin na yammacin Afirka, ta jima tana nata shiri tare da neman duk wasu masu raunannar zuciya domin su bi bayanta, ta hanyar shinfida dabaru na jan hankalin mazauna yankunan kan iyakokin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, wadanda tun ma kafin zuwan kungiyar suka sha fuskantar matsaloli na rikicin kabilanci, inda wasu ke ganin tamkar ba a yi musu shari'a ta gaskiya ba ko kuma wasu masu fada a ji suna nuna son rai wajen warware matsalolinsu.

Symbolbilder Niger Armee
Hare-haren 'yan ta'adda kan sojojin Nijar na kara yawaitaHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Al'ummar ta Jamhuriyyar Nijar dai yanzu haka na cikin rudani, biyo bayan gano wasu abubuwa masu fashewa da ke kama da rokoki a wani kauye da ake kira Kongou Zarmagandey da ke kusa da Yamai babban birnin kasar, da kuma ake zargin an so yin amfani da su ne domin kai hari birnin na Yamai. Kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar ta Nijar dai, sun yi kira da a gudanar da addu'o'i a cikin masallatai a ranar Jumma'a mai zuwa, tare kuma da yin zanga-zangar nuna goyon baya ga sojojin na Nijar bayan sallar Jumma'ar. A hannu guda kuma kowa ya zura idanu ya ga kamun ludayin sabon hafsan sojojin kasar Janar Salifou Mody wanda ya shafe shekaru a kasar Jamus. Da dama dai sun shaide shi da cewa soja ne da ya san aikinsa kuma mai son gaskiya cikin lamuransa, wanda ake ganin idan har bai gamu da katsalandan na 'yan siyasa ba, to yana iya taka rawar azo a gani a yakin da ake da masu tayar da kayar baya a kan iyakokin na Nijar.