1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya: Masu mutuwa saboda Corona sun ragu

Abdoulaye Mamane Amadou
May 3, 2020

Hukumomi a Italiya sun bayyana samun adadin wadanda suka mutu da annobar Covid-19 zuwa 174 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, adadin da ke zaman irinsa mafi kankanta tun bayan kakaba dokar kulle.

https://p.dw.com/p/3biij
Russland Moskau | Coronavirus | Test
Hoto: Getty Images/AFP/V. Maximov

Wannan lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin shiga tsarin sassauta dokar kulle domin farfado da tattalin arzikin kasar da yamu koma baya, ko da yake wasu muhimman wurare ciki har da na kananan 'yan kasuwa da gidajen cin abinci za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Firaminista Giuseppe Conte na kasar ya ce miliyoyyin ma'aikatan kasar za su iya komawa kan aiki, kana kuma akwai yiwuwar sakin tazara ga jama'ar da suke yanki daya domin fita zuwa yawon motsa jiki.

Akalla mutun dubu 29 ne suka kwanta dama a Italiyar sakamakon kamuwar da suka yi da annobar ta Covid-19.