1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya: Zanga-zangar kawo karshen yakin Ukraine

November 5, 2022

Dubban 'yan Italiya a birnin Rome sun gudanar da zanga-zangar neman a samar da zaman lafiya a Ukraine tare da mika bukata ga kasar da ta daina tura makamai don yakar Rasha.

https://p.dw.com/p/4J76S
Zanga-zanga a Italiya
Hoto: YARA NARDI/REUTERS

Masu zanga-zangar dai na rike da manya kwalaye dauke da rubutu da ke cewa 'A daina tura makamai, a kuma ba zaman lafiya dama.'

Jami'an 'yan sandan sun ce kimanin mutane dubu 30 ne suka gudanar da zanga-zangar ta wannan Asabar din. Guda daga cikin masu boren Roberto Zanotto, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, tura makamai tamkar rura wutar yakin ne da aka kwashe tsawon kimanin watanni tara ana yi.

Kasar Italiya da ke ita ma mamba ce a kungiyar kawance tsaro ta NATO na nuna goyon bayanta ga Ukraine ciki har da samar mata da makaman yaki. A jiya Juma'a ce dai ministocin harkokin wajen kungiyar G7, ciki har da Italiya suka sha alwashin ci gaba da goyon bayan Ukraine a yakin da take yi da Rasha.