Hamas na dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila
November 21, 2023Jagoran kungiyar mayakan Hamas Isma'il Haniyeh, ya sanar da cewa suna dab da kammala cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da kungiyar ke yi da Isra'ila a Zirin Gaza, lamarin da ya ba da kafar cewa Hamas din ka iya sakin Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su.
Wannan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta aike wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, inda kuma aka jiyo makamanciyar wannan sanarwa ta bakin wani jigo a kungiyar ta Hamas da wasu kasashen yamma suka ayyana a matsayin ta 'yan ta'adda, Izzet el Reshiq, lokacin da ya ke zantawa da gidan Talabijin na Al Jazeera a Talatar nan.
Karin bayani:WHO na neman a kwashe mutane daga asibitin al-Shifa na Gaza
Izzet el Reshiq ya ce nan ba da jimawa ba za su cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi da Isra'ila ta kwanaki biyar, don ba da damar shigar da kayan agaji yankin na Gaza, tare da musayar 'yan Isra'ilan da ta yi garkuwa da su a lokacin da ta kai wa Isra'ilar hari a ranar 7 ga watan Oktoban jiya, sannan ita ma Isra'ilar ta sako Falasdinawan da ke kurkukunta.
Ya kara da cewa za a ji karin bayanin batun sulhun daga hukumomin kasar Qatar da ke shiga tsakani.
Karin bayani:Matsayar Jamus a rikicin Isra'ila da Hamas
Fursunonin da Isra'ilan za ta sako su 300 ne, cikin su har da mata da kananan yara, yayin da Hamas din za ta sako mutane 50 zuwa 100 da ta kama, da suka hada da fararen hula da kuma 'yan kasashen waje, amma banda sojojin Isra'ila.