An yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar Togo
April 30, 2015Babban dan adawa a kasar Togo ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen mako wanda ya ba wa shugaba mai ci Faure Gnassingbe nasarar yin wa'adin mulki karo na uku. A ranar Laraba Jean-Pieere Fabre ya kwatanta sakamakon da zamba da ya ce ba yi daidai da abin da jam'iyyarsa ta tattara ba. Sakamakon wucin gadi da hukumar zaben Togo ta bayar a ranar Talata ya ba wa Shugaba Gnassingbe kusan kashi 60 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Ana fargaba wannan lamarin ka iya haddasa wani tashin hankali shigen wanda ya biyo bayan zaben 2005. A ranar 3 ga watan Mayu kotun tsarin mulkin kasar za ta ba da sakamakon karshe na zaben. Kungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka da kuma ECOWAS sun ce ba wata alamar aringizon kuri'u da zai sauya sakamakon zaben.