1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagoran 'yan adawa na kasar Kamaru ya rasu

Suleiman Babayo ZMA
June 13, 2023

Marigayi John Fru Ndi ya kasance wanda ya dade a matsayin jagoran 'yan adawa na kasar Kamaru kuma jam'iyyarsa ta SDF ta bayyana rasuwar.

https://p.dw.com/p/4SWl7
Lokacin zaben Kamaru
John Fru NdiHoto: dapd

Rahotanni daga kasar Kamaru sun tabbatar da rasuwar jagoran 'yan adawa na kasar John Fru Ndi, wanda ya bar duniya yana da shekaru 81 da haihuwa. Jam'iyyar marigarin ta SDF (Social Democratic Front) ta tabbatar da mutuwar cikin daren jiya Litinin.

Shi dai Marigayi John Fru Ndi ya dade yana fafata zaben shugaban kasa tare da Shugaba Paul Biya da yake rike da madafun iko fiye da shekaru 40 da suka gabata a kasar da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka. Kuma a zaben shekarar 1992 ya yi kusan lashen zaben shugaban kasar ta Kamaru amma ya yi zargin bangaren gwamnati da yi masa magudi.