Aljeriya ta sake mayar da jakada Faransa
January 5, 2022Talla
Jakadan kasar Aljeriya da ke Faransa ya koma bakin aiki bayan janye shi tun watan Okotoba da mahukuntan Aljeriya suka yi, domin nuna takaici bisa kalaman Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da suke ganin cin fuska ne ga kasar ta Aljeriya.
Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya gana da jakadan Mohamed Antar-Daoud tare da ba shi umurnin komawa bakin aiki a birnin Paris na Faransa. Ana samun tsamin dangantaka a wasu lokuta tsakanin kasashen na Faransa da Aljeriya. Ita Faransa ce ta yi wa Aljeriya mulki mallaka inda ta shafe fiye da shekaru 130 tana karkashin kasar ta Faransa kafin samun 'yanci a shekarar 1962, kimanin shekaru 60 da suka gabata.