Jakadan Faransa ya koma aikinsa a Rome
February 16, 2019Talla
Jakadan kasar Faransa ya koma kasar Italiya a ranar Juma'a inda ya bayyana cewa kasashen da ke zama makotan juna za su gyatta dangantaka da ke tsakaninsu bayan da suka shiga takaddamada ke zama mai zafi tun bayan yakin duniya na biyu. Shugaban kasar ta Italiya Sergio Mattarella shi ya karbi jakadan da ke kome a fadar shuban kasa da ke a birnin Rome.
Jakada Christian Masset ya ba da sakon wasika ga shugaban kasar ta Italiya wasikar da ke dauke da sakon gayyatar Shugaba Emmanuel Macron ga takwaransa Mattarella na Italiya zuwa birnin Paris.
A cewar ministar harkokin Faransa a kasashen Turai Nathalie Loiseau, tuni dama shugabannin kasashen biyu sun yi magana ta wayar tarho inda suka jaddada muhimmancin hadin kansu.