Jama'a na kaɗa ƙuri'a a zaɓen Iran
June 14, 2013Talla
Yanzu haka An buɗe rumfunan zaɓe a ƙasar Iran, inda jama'a suka fara kaɗa ƙuri'a domin zaɓen mutumin da zai gaji Mahmud Ahmadinejad a matsayin shugaban ƙasa wanda shi ba zai tsaya takara ba, bisa dokar ƙasar.
Mutane kimanin miliyan 50 ake sa ran za su kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen da 'yan takara shida za su kara. A ciki har da Said Jalili babban mai sasantawa na ƙasar ta Iran tsakaninta da ƙasashen yammancin duniya, a kan shirinta na nukiliya wanda kuma ke ɗaya daga cikin 'yan takarar waɗanda ake zaton za su taka rawar gani a zaɓen.
Baya ga zaɓen shugaban ƙasa dai Iraniyawan har da na 'yan majalisar dokoki da na ƙananan hukumomi za su zaɓa a yau ɗin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman