Kamen dan fafutuka a Jamhuriyar Nijar
January 24, 2023Daga zargin yada labaran neman tayar da zaune tsaye,zargin da ake wa Malam Abdoulaye Seidou shugaban kungiyar ta M62, ya rikide zuwa tayar da gobara da ke zama babban laifi a dokokin shari'ar kasar. Sai dai kawancen na M62 ya fassara matakin da bita da kulli, tare da daukar lauyoyi domin kare jagoran nasu. Takun saka tsakanin gwamnati da kawancen na 'yan fafutukar M62 din, ya samo asali ne bayan harin da 'yan ta'adda suka kai wa jami'an tsaro a garin Tamou da kuma martanin da jami'an suka mayar a ranar 24 ga watan Oktobar bara, inda a wata sanarwa da kawancen ya fitar bayan afkuwar lamarin ya zargi sojojin Nijar da aikata kisan gilla kan fararen hula da sunan 'yan ta'adda.
Bayan wannan ne hukumomin shari'a suka soma tuhumar sa da yada labari mai iya tayar da zaune tsaye a kasa, sai dai ana cikin wannan bincike ne zargin da mahukuntan ke yi wa dan fafutukar ya rikide tare da daukar sabon salo kamar dai yadda mai Shari'a Chaibou Moussa babban mai shigar da kara na gwamnatin Nijar ya bayyana a taron mema labaran da ya kira. Tuni dai kawancen na M62 ya yi watsi da wannan zargi, tare kuma da zargin babban mai shigar da karar na gwamnati da yi wa kawancen bita-da-kulli. Babban mai shigar da kara na gwamnatin kasar ta Nijar ya ce a yanzu karar, ta koma a hannun kotun shari'r manyan laifuka. Yanzu haka dai kawancen na M62 ya tsara shirya azumi a ranar Alhamis da kuma addu'o'i a Masalllatai a ranar Juma'a, cikin matakan da ya dauka na nuna rashin amincewa da wasu al'amura da ke gudana a kasar.