1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta kara kudin tallafi ga Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
July 6, 2023

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da shirin bai wa Jamhuriyar Nijar karin tallafin kudi, domin taimakon kasar a fannin tsaro da kuma ilimi.

https://p.dw.com/p/4TWKF
Tarayyar Turai | Josep Borrell | Niger
Babban jami'in kula da harkokin kasashen waje na kungiyar Tarayyar Turai Josep BorrellHoto: Sierakowski/EUC/ROPI/picture alliance

Babban jami'in kula da harkokin kasashen ketare na kungiyar ta Tarayyar Turai EU Josep Borrell ne ya sanar da hakan bayan ganawa da shugaban Jamhuriyar ta Nijar Mohamed Bazoum a fadarsa, yayin wata ziyarar aiki da Borrell din ya kai. Tuni dai al'ummar Nijar din suka fara tofa albarkacin bakinsu kan ziyarar jami'in kungiyar ta EU, wanda ya yi karin haske kan karfin huldar Tarayyar Turai da kasarsu da kuma kokarin da kungiyar ta EU ke yi domin taimakon Nijar a fannin yaki da ta'addanci da wasu fannoni na ci-gaban kasa. A watannin baya-bayan nan dai kasashen Turai na yawaita bai wa Nijar din tallafi, yayin da a hannun guda shugabannin da manyan jami'an gwamnatocin kasashen Turai ke yawaita yin zarya a kasar ko kuma kulla sababbin yarjeniyoyin tallafin kudi ko na tsaro da ita. Bayan ya halarci bikin kaddamar da sabuwar tashar samar da makamashin hasken rana a birnin Yamai, babban jami'in kungiyar ta EU Josep Borrel ya nufi birnin Agadez domin gane wa idanunsa ayyukan agajin tsaro da kungiyar ke yi a Nijar din.