Nijar ta soke dokar hukunta laifin safarar mutane zuwa Turai
November 28, 2023Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta soke dokar hukunta wadanda ake kamawa da laifin safarar mutane suna ketarawa Turai da su ta hamadar Sahara, wadda aka kafa shekarar 2015.
Wannan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar shari'ar kasar ta fitar, mai dauke da sa hannun babban sakatarenta Ibrahim Jean Etienne, bayan amincewar shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdourahmane Tchiani, kuma wadanda suke daure yanzu haka a kan laifin to za a sake su.
Karin bayani:Shugaban Nijar na ziyarar aiki a Mali da Burkina Faso
Wannan matakin na gwamnatin sojin Nijar din ka iya kara janyo takun saka tsakaninta da kasashen Turai da suka kakaba mata takunkumi, sakamakon hambarar da gwamnatin dimukuradiyya ta Mohamed Bazoum a cikin watan Yulin bana.
Karin bayani:Karar da Jamhuriyra Nijar ta shigar kotun ECOWAS
Yankin Agadez na Jamhuriyar Nijar na zama wata babbar kofar ficewa zuwa Turai ta hanyar shiga Libya, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa a duk mako daya akalla 'yan ci-rani dubu arba'in ne suke bi ta Agadez don shiga Turai ba bisa ka'ida ba.