COVID-19: Nijar na zaman makoki
May 4, 2020An haifi Mohamed Ben Omar ne a ranar huduga watan Janairun shekara ta 1965 a garin Tasker da ke gundumar Goure a jihar Damagaram. Shi dai marigayi Ben Omar kafin rasuwarsa ya kasance shugaban jam'iyyar PSD Bassira, ya kuma rike mukaman minista da dama. Kafin shigarsa siyasa, Ben Omar malamin makaranta ne wanda daga shekara ta 2000 zuwa 2004 ya koyar da darasin tarihi da labarin kasa a nan birnin Yamai.
Mukaman siyasa da dama
Daga shekara ta 2004 zuwa 2007, an nada shi a matsayin minista mai kula da hulda tsakanin manyan ma'aikatu na gwamnati, ya kuma zamo minista mai magana da yawun gamnati daga shekara ta 2007 zuwa 2009.
Marigayi Ben Omar Mohamed ya zama dan majalisar dokoki ta kasa, inda daga ranar 14 ga watan Nuwambar shekara ta 2009 zuwa 18 ga watan Febrairun shekara ta 2010, ya kasance mataimaki na hudu na shugaban majalisar dokoki a karkashin jamhuriya ta shida mai gajeran zongo. Sannan daga watan Maris na 2011 zuwa Afrilun 2016 Ben Omar ya sake zama mataimaki na hudu na shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar a karkashin jamhuriya ta bakwai.
Ya rike ministan ilimi mai zurfi na tsawon shekara guda daga watan Afrilu na 2016 zuwa Afrilun 2017, inda tun daga ranar 27 ga watan Afrilun 2017 din ya ke rike da mukamin ministan ma'aikatan kwadago.
Coronavirus ce sila
Marigayin ya kirkiro jam'iyyar siyasa mai suna PSD Bassira a ranar 15 ga watan Disamba na 2015, inda ya kasance shugaban jam'iyyar. Shi dai Ben Omar ya fito ne daga cikin kabilar Larabawa na garin Tesker gundumar Goure, cikin jihar Damagaram. Rahotanni sun nunar da cewa, dama Ben Omar na da hawan jini, abin da ya baiwaa annobar Coronavirus damar saurin samun galaba a kansa tare da yi masa kwaf daya. Ben Omar Ya rasu ya bar mace guda da 'ya'ya shida biyu mata hudu maza.
An yi jana'izar marigayin ne a makabartar Musulmi ta Yantala, inda Shugfaba Issoufou Mahamadou ya samu halarta tare da sauran ministoci da 'yan majalisar dokokin kasar.