1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam´iyun adawa a ƙasar Guine-Conakry sun buƙaci a girka gwamnatin riƙwan ƙwarya

March 21, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4Q

Jam´iyun adawa a ƙasar Guine Konakry, sun buƙaci a girka gwamnatin rikwan kwarya a dalilin da rashin lahiyar da shugaban ƙasar Lansana Konte, ke fama da ita.

A yanzu haka, shugaban na kwance a wata asibitin ƙurraru da ke ƙasar Suizland.

Lansana Konte, ya daɗe, ya na fama matsanciyar cutar ciwon sukari.

Masu kulla da harakokin siyasa a wannan ƙasa, sun fara hasashen sojoji, su yi anfani da wannan dama, domin aiwatar da juyin mulki.

A cikin sanarwar da su ka hiddo a yau, yan adawar Guine-Konacry, sun yi dogaro da sakamakon tantanawar da aki yi, tsakanin jami´yun adawa, da ƙungiyoyin fara hulla, wanda shima, ya bayyana wannan buƙata.

Sun bada shawara girka gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta tsawan watani 18, wace za a ɗorawa yaunin shirya zaɓe, da kuma wata hukuma, da za ta ƙunshi wakilan jam´iyun ƙasar baki ɗaya, da ƙungiyoyin fara hulla, wadda za ta maye gurbin majalisar dokoki.

Saidai wata sanarwa da opishin jikadancin Guine, a ƙasar Suizland ta hiddo a sahiyar yau ta bayyana cewar shugaba Lansana Konte ya fara samun sauƙi.