Jam'iyun Jamus na adawa da goyon bayan Merkel ga Sarkozy.
February 7, 2012Jam'iyun adawan ƙasar Jamus na ci gaba da sukar yunƙurin shugabar gwamnati Angela Merkel na dafa wa Nicholas Sarkozy Baya, a ƙoƙarin da ya ke yi na neman lashe wa'adin mulkin faransa a karo na biyu. Shugaban masu rajin kare muhalli a majalisar dokoki ta Bundestag, wato Juergen Tritin ya bayyana cewa goyon bayan da shugabar jam'iyar CDU mai mulkin Jamus ke bai wa shugaba Sarkozy da farin jininsa ke raguwa, zai iya kawo rauni ga dangartakar da ke tsakanin Jamus da Faransa.
Ita ma dai jam'iyar SPD da ke da ra'ayin gurguzu ta soki lamirin Merkel na amfani da taro tsakanin gwamnatocin ƙasasehen biyu wajen taya sarkozy gudanar da yaƙin nerman zaɓe. A lokacin da ta ke mayar da martani mataimakiyar shugabar SPD, kana gwamnar jihar NordRhein-Westefallen wato Hannalore Kraft ta ce jam'iyarta za ta fito fili ta mara wa ɗan takaran jam'iyar gurguzu ta Faransa wato Francois Holland baya. Ranar 22 ga watan afrilu ne dai za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban ƙasa a ƙasar ta Faransa. Yayin da zagaye na biyu kuma, zai gudana makwani biyu bayan zagayen na farko tsakanin 'yan takara da suka zo na daya da kuma na biyu.
Mwallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Ahmad Tijjani Lawal