1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

291012 Ukraine Wahlen

Zainab MohammedOctober 29, 2012

Sakamakon farko na zaɓen 'yan majalisar wakilai da aka gudanar a ƙarshen mako, ya nuna jam'iyyar da ke mulki da sauran jam'iyyun adawar Ukraine ɗin sun taka rawar gani.

https://p.dw.com/p/16Z3k
Members of a local electoral commission empty a ballot box at a polling station after voting day in Kiev October 28, 2012. Ukrainian President Viktor Yanukovich's pro-business party seemed likely to hold on to a majority in parliament after an election on Sunday, but it will face a revitalised opposition boosted by a resurgent nationalist party, exit polls showed. REUTERS/Gleb Garanich (UKRAINE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Priminista Mykola Azarov, ya sanar da cewar jam'iyyr dake mulkin ƙasar a yanzu zata lashe zaɓen da mafi rinjayen kujeru a sabuwar majalisar wakilai, bisa ga zaɓen na ranar lahadi, da ƙasashwen yammaci na turai kewa kallon zakaran gwajin dafi wa Democraɗiyyar wannan ƙasa dake fuskantar ruɗani sakamakon tsare tsohuwar Priminista Julia Tymoshenko.

Ayayinda jam'iyyar adawa ta Tymoshenko ta samu ɗaukaka, ita kuwa jam'iyyar fitaccen ɗan danben nan Vitali Klitschko, ta gaza samun nasarar da ake saran zata samu, kana jam'iyyar ɗan kwallo Andriy Shevchenko ta ruguje kasa warwas.

Vitali Klitscho yayi maraba da wannan nasara da jam'iyyarsa ke samu bisa ga sakamakon.

epa03451190 Ukrainian heavyweight boxing champion and leader of political party UDAR Vitaly Klitschko speaks with media during his press conference in Kiev, Ukraine, 29 October 2012. With some 42.79 per cent of the vote in 28 October election counted, the pro-Russian Regions Ukraine party of President Viktor Yanukovych won 35.3 per cent of the vote, the Central Election Commission said. The party's Communist allies meanwhile won 15 percent. Opposition Motherland party, headed by jailed former Premier Yulia Tymoshenko, received 21.7 percent of the vote. UDAR, a party led by boxing champion Vitali Klitschko, got around 12.8 percent, and the nationalist Freedom party, 8.1 percent. EPA/SERGEY DOLZHENKO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Vitali KlitschkoHoto: picture-alliance/dpa

Ya ce " bisa ga sakamakon da aka samu, jam'iyyarmu ce ta uku a yawan goyon bayan masu zaɓe. A ganina wannan sakamako abun maraba ne a ɓangaren wannan jaririyar jam'iyya tamu, kuma nayi imanin cewar zamu samu karin kuri'u, kuma zamu nuna bajinta da sanin yakamata a ayyukanmu a majalisa".

Sanarawar hukumar zaɓen ƙasar dai na nuni da cewar, Jam'iyyar Regions ta shugaba Victor Yanukovych ta samu kashi 35.03, a yayin da jam'iyyar adawa ta Tymoshenko ta samu kashi 21.98 daga cikin 100, bisa ga yawan ƙuri'u da aka kidaya ya zuwa wannan litinin.

Manazarta dai sun yi hasashen cewar jam'iyyar dake mulkin Ukraine zata lashe kujeru 114 daga cikin yawan kujeru 225 dake rukunin mazaɓun da zaka tsaya domin a zaɓe ka.

Jam'iyyar masu kishin ƙasa ta Ukraine ta swoda a karon farko ta samu karɓuwa inda ta samu kashi 7 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kaɗa a zaɓen na ranar lahadi. Sai dai shugaban Jam'iyyar Oleh Tyahnybok yana mai ra'ayin cewar ba girin ba wai dai tayi mai.

Yace " ya kamata mu jira tukuna, bai kamata mu fara bukukuwan samun nasara ba. Domin idan muka fara bukukuwa yanzu komai zai iya faruwa, sakamakon zai iya sauyawa, za'a iya zaftare rabin kuri'un da muka samu. Wannan ba ƙasar demokraɗiyya bace, kamar yadda yake a sauran ƙasashen Turai. Komai na iya faruwa a ƙasar Ukrain".

Acewar Olexander Efremov dake shugabantar 'yan majalisar jam'iyyar dake mulki ta Regions, zasu lashe kujeru 230 daga cikin yawan kujeru 450 a sabuwar majalisar. Hakan kuwa a cewar majiyar jam'iyyar zai samu ne ko a matakin zaben ɗan takara, ko kuma da tallafin rinjayen da jam'iyyarsu zata samu a zaɓen.

epa03450544 Prisoners of Kachanivska prison, where former Ukrainian Prime Minister and opposition leader Yulia Tymoshenkois is jailed, cast their ballots during parliamentary elections in Kharkiv, Ukraine, 28 October 2012. Voting began Sunday morning in Ukrainian parliamentary elections that opinion polls showed would deliver a reinvigorated opposition for the government as it faces charges of corruption and authoritarianism. Polling centres opened at 8 am (0600 GMT) and would close 12 hours later for the 36.6 million eligible voters to chose between the government side, led by President Viktor Yanukovych, and a united opposition, led by heavyweight boxing champion Vitali Klitschko and former prime minister Yulia Tymoshenko. EPA/SERGEY KOZLOV +++(c) dpa - Bildfunk+++
Masu zaɓeHoto: picture-alliance/dpa

An kiyasta cewar kashi 58 daga cikin 100 na yawan wadanda suka cancanci kaɗa kuriU suka fita domin gudanar da zaɓen 'yan majalisar na Ukraine a ranar lahadi.

Hankalin Rasha dai na kan yadda sakamakon zaɓen, kazalika Tarayyar Turai, wadda ke ƙoƙarin tabbatar da ganin cewar an bi tsarin demokraɗiyya na tsantsa, musamman ayayinda Kiev ke ci gaba da nuna muradin hadewa a gamayyar ƙungiyar ta EU.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu