1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar jam'iyyar AfD a Berlin

Salissou Boukari
May 27, 2018

Birnin Berlin da ke zamanfadar gwamnatin Jamus ya fuskanci jerin zanga-zanga ta 'yan jam'iyyar AfD masu kyamar baki, da kuma zanga-zangar masu adawa da akidar 'yan jamiyyar ta AfD.

https://p.dw.com/p/2yPY9
Protest gegen AfD-Demonstration
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

'Yan jam'iyar ta AfD dai sun yi jerin gwanon ne tun daga babbar tashar jiragen kasa har ya zuwa kofar Brandenburg da ke kusa da majalisar dokokin kasar ta Bundestag, inda suke furta kalamai na cewa "Merkel ta fice", sannan wasu na cewa "mu ne al'umma". Daga bangare daya kuma kusa da cibiyar majalisar dokokin ta Jamus dubban masu nuna adawa da masu kyamar bakin ne suka fito, da suka hada da 'yan kungiyoyi daban-daban masu zaman kansu gami da jam'iyyun siyasa da ma mazauna birnin na Berlin, inda su ma suka yi nasu jerin gwanon wanda sai da suka tilaswa 'yan jam'iyyar ta AfD sauya hanyar da ta kamata su bi sakamakon toshe wata gada da masu zanga-zangar adawa da nuna wariyar suka yi.

Jam'iyyar AfD ta masu kyamar bakin a nan Jamus dai, ta ce an jefi daya daga cikin motocinta na Bus da ruwan fenti da kuma duwatsu, sannan daga nasu bangare jami'an tsaro na 'yan sanda sun ce sai da suka yi amfani da gas mai sa kaikayin jiki wajen shiga tsakanin bangarorin biyu masu zanga-zanga a wasu wuraran. Gabaki daya dai an tanadi 'yan sanda kimanin 2,000 domin bada kariya ga zanga-zangar.