1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kramp-Karrenbauer ta gaji Merkel a jagorancin CDU

December 7, 2018

Jam'iyyar CDU mai mulkin Jamus ta zabi Annegret Kramp-Karrenbauer a matsayin wadda za ta gaji Angela Merkel a jagorancin jam'iyyar.

https://p.dw.com/p/39gSy
Deutschland CDU-Parteitag in Hamburg Kramp-Karrenbauer und Merkel
Hoto: Reuters/F. Bimmer

Wakilan jam'iyyar CDU mai mulkin Jamus sun zabi Annegret Kramp-Karrenbauer a matsayin wadda za ta gaji Angela Merkel a jagorancin jam'iyyar.

Annegret Kramp-Karrenbauer, wacce babbar ta hannun damar shugabar gwamnati Angela Merkel ce ta ci zaben da aka yi a birnin Hamburg ne da kuri'u 517.

Daga cikin kuri'u 999 da wakilan jam'iyyar suka kada, hamshakin attajirin nan kuma lauya, Friedrich Merz, shi ne ya zo na biyu da kuri'u 482.

Ministan lafiya Jens Spahn, wanda ya zo na uku a fafatawar, ya fita ne a zagayen farko na zaben wanda aka yi a wannan Juma'a.  

Nasarar zama jagora a jam'iyyar CDU, na nufin damar samun shugabancin gwamnatin Jamus ke nan bayan shugabar gwamnati Angela Merkel ta sauka daga karagar mulki a shekara ta 2021.