CDU na yin taro domin samun magadin Merkel
January 15, 2021Lokacin da Jamusawa za su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin tarayyar a karshen wannan shekara, zai kasance shugabar gwamnati Angela Merkel, ta shafe shekaru 16 a kan wannan mukami. Ta yi zamani da shugabannin uku na Amirka da firaministoci biyar na Birtaniya da bakwai na Italiya. Ta kuma tsallake matsaloli da dama da aka fuskanta a tsukin wanan lokaci, kama daga mtasalolin bashi a Turai ya zuwa annobar Corona.
Ko da yake a hukumance a babban taron jam'iyyar ta CDU da zai gudana ta kafar intanet ba batun wanda zai gaji Merkel za a duba ba, abin da zai dauki hankali shi ne shugabann jam'iyya, amma kasance a binciken jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan jam'iyyar ce ke kan gaba, a dole za a duba batun wanda zai iya zama shugaban gwamnati.
'Yan takara uku ke neman kujerar shugabanci na jam'iyyar ta CDU
'Yan takara uku da ke neman kujerar shugabancin CDU, su ne Friedrich Merz tsohon shugaban bangaren jam'iyyun CDU CSU a majalisar dokoki, da firimiyan Jihar North Rhein Westfalia Armin Laschet sai kuma Nobert Röttgen masanin manufar ketare ta Jamus.
Dukkan su uku magidanta ne 'yan darikar Katholika daga Jihar North Rhein Westfalia, suna kuma da matsakaicin ra'ayi. Suna kuma suna damuwa game da makomar jam'iyyar musamman dangane da sauye-sauye na zamantakewa da baki, kamar yadda Armin Laschet da ke ba da muhimmanci kan adalci da tsaron cikin gida ya nunar. Ya ce: "Dole mu tambayi kanmu, shin a matsayinmu na CDU muna wakiltar wannan jama'a kuwa. Amsa dai ita ce a'a. Idan kuma muka gamsar da baki muka jawo su garemu muna da wata dama ta ci gaba da zama jam'iyyar al'umma."
Ra'ayin fafutukar kare muhali daga dukkanin 'yan takara guda uku
Dukkan 'yan takarar uku na son karfafa fasahar digital da kare muhalli da kuma bunkasa tattalin arzikin Jamus. Sai dai a nasa bangaren Norbert Röttgen shugaban kiwamitin harkokinn ketare a majalisar dokoki yana son Jamus ta kara daukar nauyi a harkokin siyasa na Turai da duniya baki daya. Ya ce: "Jam'iyyarmu jam'iyya ce ta duniya, jam'iyya ce ta Turai jam'iyya ce kuma ta dangantaka tsakanin Turai da Amirka. Dole mu kara karfafa ta." Friedrich Merz da ake wa kallon wakilin kamfanoni yana goyon bayan karfafa manufofi na 'yan ra'ayin mazan jiya, wanda masu tallafa masa ke sa rai zai jawo masu zabe daga jam'iyyar AfD. Ana kuma gani zai aiwatar da canje-canje a cikin jam'iyyar ta CDU, inda ma ya yi kiran ga jam'iyyar da ta bi sahun Merkel, yana mai cewa kyakkyawan matakan da ta dauka na yaki da Corona sun kara wa CDU tagomashi. Ya ce: "A ranar 26 ga watan Satumba za mu kada kuri'a ba saboda mika godiya bisa abubuwan da suka faru a baya ba, amma za mu sa rai mu kuma yi kyakkyawan fata ga makomarmu."
Yanzu haka dai Laschet ne kadai ke cikin gwamnati, Merz ya taba rike mukami, a 2012 Merkel ta sallami Röttgen daga mukamin ministan muhalli. Sai dai kuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna Merz na da kashi 30 cikin 100 yayin da Röttgen da Laschet kowanensu ke da kashi 25 cikin 100 na magoya bayan