SiyasaJamus
Jam'iyya mai mulki ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki
June 15, 2021Talla
Jam'iyyar FLN ta kasar Aljeriya ta lashe akasarin kujeru a zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Hukumar zaben kasar ce ta sanar da hakan, sai dai duk da wannan nasarar, tana bukatar karin kuri'u kafin ta sami rinjaye a halin da ake ciki a kasar da ta sha fama da zanga-zangar neman sauyi.
Jam'iyyar ta FLN ta yi ma sauran fintinkau bayan da ta sami kujeru 105, Jam'iyyar Independent Candidates ta sami kujeru 78 a yayin da jam'iyyar MSP ta sami kujeru sittin da hudu. Ana bukatar kimanin samun kujeru 204 daga cikin 407 kafin jam'iyya ta sami rinjaye a majalisar kasar ta Aljeriya. Masana na ganin da wuya zaben 'yan majalisar dokoki, ya yi tasirin kawo canji a dimukuradiyyar kasar.