Jam'iyyar MPLA na shirin lashe zaben Angola
August 26, 2022Talla
Daga cikin kaso 97 cikin dari na sakamakon da aka kidanya, rahotanni na nuni da cewa Shugaba Joao Lourenco ya sami kaso 51 cikin dari a cewar hukumar zaben kasar.
Ita kuma a nata bangaren jam'iyyar adawa ta UNITA ta sami kaso 44 cikin dari na kuri'un da aka kai ga kirgawa. yayin da kananan jam'iyyu da ke rufa musu baya ke da sauran kason.
An sami karancin wadanda suka kada kuri'unsu a wannan zaben. Inda hukumar zabe mai zaman kanta tace kaso 45 na al'ummar kasar ne suka yi rajista zaben tun da farko, matakin da ke nuni da koma baya idan aka kwatanta da zaben da ya gabata.
Jam'iyyun MPLA mai mulki da UNITA dai, sun kwashe tsawon shekaru suna hamayya da juna tun gabanin samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka da kasar ta Angola ta yi.