Jam'iyyar Socialist ta ci zabe a Spain
April 29, 2019Talla
Jam'iyyar Socialist ta firaministan Spain, Pedro Sanchez, ta lashe zaben kasar da dan karamin rinjaye, inda za ta mulki kasar mai majalisar da ke dauke da masu tsaurin ra'ayi. Jam'iyyar ta sami kujeru 123 cikin 350 abin da ke matsayin kashi 29 na kuri'n da aka kada.
Sakamakon zaben na nunin cewa kasar ta Spain na kan hanyar shiga wani sabon babi ne na rigingimun siyasa.
Sai dai hakan na nunin tasiri ne kan yadda ta samu a zaben shekarar 2016, inda ta tashi da kujeru 85.
Shugaba Sanchez dai na dogaro ne da hadin gwiwar da ke iya samuwa daga masu zafin adawa, tun bayan rashin nasarar ballewar yankin Kataloniya a shekara ta 2017.