1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

PDP za ta dauki mataki a kan hukuncin kotu

Binta Aliyu Zurmi
September 7, 2023

Jam'iyyun adawar Najeriya PDP da LP sun yi fatali da hukunci da kotun sauraren kararakin zabe ta yanke na tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

https://p.dw.com/p/4W2ro
Nigeria Wahlen 2023/Präsidentschaftskandidat Atiku Abubakar
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Biyo bayan hukuncin da kotun sauraren kararakin zaben shekarar 2023 ta yanke a birnin Abuja.

A wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta fidda a daren jiya, ta ce bayan dogon nazari da suka yi wa hukuncin, sun gano kura-kurai da aka tafka wajen yanke shi, kuma za su dauki mataki na gaba. Dama jam'iyyar ta PDP ta sha alwashin kalubalantar sakamakon zaben tun da farko.

Ita ma a nata bangaren jam'iyyar Labour Party ta Peter Obi ta yi watsi da hukuncin, inda ta ce ba a yi adalci da ma bin muradun al'ummar kasar ba.

A ranar Laraba ne kotun sauraren kararakin zaben shugaban kasa ta yi zamanta na karshe a kan kararrakin da aka shigar gabanta, bayan kwashe sa'o'i sama da 12 ta yanke hukuncin tabbatar da nasarar da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.