1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jam'iyyun hadaka a Jamus sun gaza a zaben Bavaria da Hesse

October 9, 2023

Hadakar jam'iyyu masu mulki a Jamus, sun fuskanci koma baya a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi a cikin jihohin Bavaria da kuma Hesse masu yawan al'uma.

https://p.dw.com/p/4XHS0
Firimiyan jihar Bavaria, Markus Söder
Firimiyan jihar Bavaria, Markus Söder Hoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP

Jami'yya mai rajin kare muradun talakawa ta AfD, ta samu nasarar da ba ta taba samu ba a tarihi a jihar Hesse.

Jam'iyyar ta AfD da bisa al'ada ke da karfi a gabashin Jamus, ta zo ta biyu a zaben da aka yi a jihohin na Bavaria da Hesse.

Dukkanin jam'iyyun da suka hadu suka kafa gwamnati a Jamus, wato da Social Democrats da jam'iyyar the Greens gami da Free Democrats (FDP), sun yi mumunar faduwar da ba su yi ba cikin shekaru biyar.

Jihohin na Hesse da Bavaria dai na da kashi daya bisa hudu na yawan al'umar kasar Jamus baki daya.

Firimiyar jihar Bavarian kuma dan takarar jam'iyyar CSU, Markus Söder ya ce jiharsa ta zabi ƙarko a wannan karon.