Jamus: An amince da dokar auren jinsi
June 30, 2017Wannan doka dai yanzu ta saka Jamus cikin jerin wasu manyan kasashen yammaci da tuni suka dade da aiwatar da dokar, duk da cewar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ba abin da ta zaba ba ke'nan, amma hakan bai sa ta kawo tsaiko wajen mika dokar zuwa gaba ba. 'Yan Majalisa kimanin 393 ne dai suka amince da dokar ta auren jinsi guda sannan 226 kuma suka watsi da ita, yayin da hudu kuma suka kauracewa kada kuri'ar. Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta bayyana dalilin da ya sa ta ki zabar amincewa da dokar.
Ta ce:'' bisa ga yadda kundin tsarin mulkin kasa ya bayyana aure shi ne tsakanin mace da namiji wannan ne kuma dalilin da ya sa ban zabi amincewa da dokar ba a yau.'' A watan Afirilun shekara ta 2001 ne dai kasar Holland ta zamo kasa ta farko a duniya da ta amince da dokar auren jinsi wadda har ta ba su damar gudanar da biki kamar yadda ake yi lokacin da aka yi aure tsakanin mace da namiji. Kasashe kimanin goma sha biyu ne dai a Turai a yanzu haka suke da irin wannan dokar. Yanzu haka dai ana sa ran nan da karshen wannan shekara ta 2017 dokar za ta fara aiki gadan-gadan a Jamus.