Kotun Stuttgart ta ci kamfanin Porsche tara
October 24, 2018A nan kasar Jamus wata kotun birnin Stuttgart ta ci kamfanin kera motoci na Porche tarar kudi miliyan 47 na Euro a matsayin na kisan laifi ga mutanen da ya yaudara ta hanyar sayar masu da motocin masu injin jabu da ke boye gaskiyar yawan gurbataccen hayakin da yake fitarwa.
Kotun ta yanke wa kamfanin na Porsche wannan hukunci bayan da ta same shi da laifin yin jinkiri wajen ankarar da jama'a kan matsalar da ke tattare da injin motocin kamfanin na Porsche da ke da rnjaye hannun jari a kamfanin kera motocin sanfarin Volkswagen.
Mutanen da suka kalubalancin kamfanin a gaban kuliya dai sun bukaci a biya su kudin kisan laifi da yawansu ya kai miliyan 164 na Euro.Sai dai kamfanin na Porsche ya sanar da shirin daukaka kara kan wannan hukunci na kotu.