Jamus: An samu dan Siriya da laifin garkuwa
October 16, 2018Babban Jami'in 'yan sandan birnin Kolon Klaus-Stephen Becker ya shaidawa manema labarai yadda mutumin yayi yunkurun kunna wuta a gidan abinci na McDonald dake babbar tashar jirgin kasan birnin na Kolon kafin yayi garkiwa da wata mace dake tsaka da aiki a wani kantin sayar da magunguna. Binciken da jami'an tsaro suka gudanar ya tabbatar da cewar mutumin wanda ya shigo Jamus a shekara ta 2015 kuma a halin yanzu yake da shaidar ci gaba da zama a kasar har zuwa shekara ta 2021 na da alaka da kungiyar ta'adda ta IS.
A wani sabon labarin kuma mataimakiyar shugaban hukumar 'yan sanda a Kolon Miriam Brauns ta bayyana cewar duk da jami'an tsaro sun yi nasarar harbinsa a lokacin da suke yunkurin cafke shi, a halin da ake ciki yana taimakawa jami'an tsaro da bayanai.