1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron taimakon Ukraine da makaman yaki

Ramatu Garba Baba LMJ
January 20, 2023

Wasu daga cikin kasashen yamma suna dari-darin taimakon Ukraine da makaman yakin da shugaban kasar ya nemi a ba shi, domin kare kasarsa daga munanan hare-haren Rasha.

https://p.dw.com/p/4MUzd
Shugaba Volodymr Zelensky a taron ta bidiyo
Shugaba Volodymr Zelensky a taron ta bidiyoHoto: Wolfgang Rattay/REUTERS

Ministocin tsaron kasashen yamma sun kamalla taro na yini guda, cike da shakku kan yiwuwar ganin nasarar Ukraine a kan Rasha. Amirka ta ce, abu ne mai wuya Ukraine ta cimma burinta a cikin wannan shekarar. A jawabinsa yayin taron, sakataren tsaron Amirka Lloyd Austin ya ce akwai bukatar hada karfi da karfe a kuma amince da murya guda kan mahinmancin wadata kasar da makaman da take bukata domin kare kanta daga mamayar Rasha.Kasashe kimanin 50 ne dai, suka tura wakilansu zuwa taron da ke gudana a sansanin sojojin sama na Ramstein.

A nasa jawabin Shugaba Volodymr Zelensky da ya halarci taron ta bidiyo ya bayyana damuwarsa yana mai cewa, yakin da suke da Rasha babban kalubale ne ba ma ga kasarsa kadai ba har ma da duniya baki daya. A cewarsa, akwai bukatar a mara masa baya. Kawunan shugabanin kasashen duniya sun rarrabu kan aike manyan tankokin yaki kira Leopard da ake kerawa a Jamuus da Ukraine ke da matukar bukatarsu, wasu na ganin hakan ba ya rasa nasaba da barazanar da Rasha ta yi na tsananta hare-hare tare da lalata makaman da za a bai wa Ukraine din tallafi.