1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin Siriya: Jamus na ja da baya

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 8, 2019

Kakakin gwamnatin Jamus ya sanar da cewa kasarsa ba za ta tura sojojinta na kasa domin yakar 'yan ta'adda masu kaifin kishin addini a Siriya ba.

https://p.dw.com/p/3LkyV
Bundeswehr Patriot Einsatz Türkei Raketenabwehrstaffeln
Sojojin Jamus na atisaye a kan iyakar Siriya da TurkiyyaHoto: Sean Gallup/Getty Images

A baya dai Jamus din ta tura sojojinta, inda suka taka rawa a cikin rundunar taron dangi karkashin jagorancin Amirka, ta hanyar zuba mai a jiragen yaki da kuma bayar da horo ga dakarun sojan kasar Iraqi. Wannan tsarin dai da Jamus din ke ciki na zuwa karshe ne a watan Oktobar wannan shekarar. Babban wakilin Amirka a Siriyan James Jeffrey ne dai ya bukaci Jamus din da ta tura sojojinta na kasa domin su maye gurbin na kasarsa da ke shirin kammala ficewa daga Siriyan baki daya.