1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahukunta ba za su dauki matakai

Zainab Mohammed Abubakar
March 20, 2021

Angela Merkel ta ce, mahukunta ba za su yi kasa a gwiwa wajen tsaurara dokokin yaki da corona da sake garkame kasar idan bukatar hakan ta taso ba.

https://p.dw.com/p/3qtpw
Deutschland Angela Merkel
Hoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus din ta yi wannan furucin ne bayan ganawa da gwamnonin jihohin tarayyar kasar dangane da tafiyar hawainiyar da shirin allurar rigakafin corona ke yi.

Mahukuntan tarayya da na jihohin dai sun cimma matsayar kafa dokar hana fita mai tsauri, a wani mataki na dakile kara yaduwar da cutar, idan har aka sake samun yanayin da mutane 100 daga cikin dubu 100 na kamuwa da cutar a cikin mako guda.

Jamus din dai na fuskantar zagaye na uku na annobar COVID, a yayin da sabon nau'in cutar mai asali daga Birtaniya ke yaduwa tsakanin jama'a, kamar wutar jeji.