1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar Greens ta sami tagomashi a zaben Turai

Abdoulaye Mamane Amadou
May 26, 2019

Kawancen jam'iyyun da ke mulki a Tarayyar Jamus na kan gaba da 'yar tazara a zaben 'yan majalisun dokokin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da aka gudanar a Jamus da sauran wasu kasashen kungiyar.

https://p.dw.com/p/3J83I
Deutschland Berlin | Reaktion Grüne Europawahl
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Kawancen jam'iyyun CDU da CSU dake mulki a nan Jamus na kan gaba a zaben da aka gudanar na 'yan majalisun dokokin Kungiyar Tarayyar Turai a yau Lahadi.

Wannan matsayin na zuwa ne duk da raguwar da ake ganin kawancen ya samu a wannan karo inda ya samu kaso 28,3%  kawai na adadin kuri'un da aka kada. 

Deutschland | Bürgerschaftswahl Bremen | Robert Habeck (Grüne)
Robert Habeck na jam'iyyar Greens Hoto: picture-alliance/dpa/C. Jaspersen

Sai dai kididdiga ta yi nuni da cewar jam'iyyar masu rajin kare muhalli "The Greens" ta samu karin ci gaba fiye da yadda aka zata, inda ta samu kaso 20,5% sabanin kashi 10,7%  da ta samu a shekarar 2014.  

Ita ma dai AfD ta masu kyamar baki ta cimma burinta da kaso 10,5 sabanin kashi 7,1 da ta samu a 2014 a yayin da ita kuwa SPD  ta masu ra'ayin gurguzu kana mamba a kawancen masu mulki ta tashi da kaso 15,5% na kuri'un.

A wannan Lahadin ce dai galibin kasashen Kungiyar ta Tarayyar Turai suka jefa kuri'a don zabar 'yan majalisun dokoki fiye da 750 da za su kasance mambobin majalisar dokokin ta EU.