1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron kara bude hanyoyin saka hannun jarin Jamusawa a Afirka

Usman Shehu Usman AMA
August 27, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi ganawar karshe da wasu shugabannin Afirka a taron koli na karfafa huldar tattalin arziki tsakanin Jamus da nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3zZiN
Händeschütteln Bundeskanzlerin Angela Merkel und Vorsitzender Kommission Afrikanische Union (AU) Moussa Faki
Merkel na musabaha da Moussa Faki, shugaban Kungiyar Tarayyar AfirkaHoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP/Getty Images

Shugabannin Afirka da dama sun halarci zauren taron a birnin Berlin kana wasu kuma suka kasance ta hanyar bidiyo, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merk ta fitar jadawali masu yawa kan nahiyar Afirka a tsawon shekarun da ta yi tana mulkin kasar Jamus, wani daga cikin shirinta na baya-bayannan shi ne "Compact with Africa Initiative" wanda ya kunshi tsarin gwamnatin Jamus na tallafawa kamfanoni masu bukatar zuba jari a Afirka.

A cewar Christoph Kannengießer shugaban kungiyar Jamusawa masu kasuwanci da Afirka, akwai matukar ci-gaba a tsakanin huldar Jamus da nahiyar Afirka, yana mai cewa "Kamfanonin Jamus da dama da ke harkokinsu a Afirka musamman masu matsakaitan masana’antu, kuma zuba jarin kamfanonin ya shafi fannoni masu yawa, idan muka yi misali da shekarar 2018 zuwa 2019 gabanin corona, kamfanonin Jamus sun karu a Afirka da kaso 10 cikin dari." Sabon tsarin hulda da Afirka wanda kasar Jamus ta fitar lokacin da ta karbi shugabancin kungiyar G20, an yi shi ne musamman don gwamnati ta bude wata kofa wa kamfanonin Jamus da ke son yin kasuwanci a Afirka. 

Berlin Bundeskanzlerin Angela Merkel und ivorischer Präsident Alassane Ouattara
Alassane Ouattara da Merkel sun sake tozaliHoto: JOHN MACDOUGALL/AFP/Getty Images

Sai dai akwai sabanin ra'ayi kan wannan, wasu na cewa ya yi nasara wasu kuwa na cewa ba a dukkan Afirka ba ne tsarin ya yi aiki kana kuma Olumide Abimbola, daraktan wata kungiyar mai kare muradun Afirka da ke birnin Berlin ne "Idan mutuum ya duba muka duba lokacin da shugabar gwamnati ta yi wannan furucin, a Afirka banga wani karin zuba jari mai yawa ba, akwai dai-daikun kasashen da suka samu karin kamfanonin Jamus a misali a kudancin Afirka akwai kasar Afrika ta Kudu da Najeriya a yammacin Afirka da kuma watakila Ghana da Kenya a gabashin Afirka."

Daga shekara 2017 zuwa 2019, kamfanonin Jamus sun zuba jari na Euro Biliyan daya da miliyan 57 a nahiyar Afirka, wanda shi ne lisafin da ake da shi bayan fidda tsarin da Merkel ta yi kan nahiyar Afirka, sai dai  kuma a cewa Abimbola, tun lokacin da Jamus ta fitar tasrin iganta huldarta da Afirka, ana iya cewa dai-daikun kasashe ne kawai suka ci gajiyar shirin. 

 Ba makawa annobar conrona ta kawo cikas ga tsarin na gwamnatin Jamus, domin shekaru biyu kenan babu wata cikakkar hakar kasuwanci tsakanin kasa da kasa, musamman ta bangare zuba sabon jari. Ko da yake a shkarar 2019 gabanin yaduwar corona sama da kamfanonin Jamus 884 da suke a Afirka, wato karin kafamnoni 42 bayan fitar da tsarin na gwamnatin Merkel. Wannan haduwar ita ce ta karshe a matsayin sallama da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wa shugabannin nahiyar Afirka.