Sabunta dangantakar Jamus da Birtaniya
July 2, 2021Talla
Firaminstan Birtaniya Boris Johnson da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ne suka sanar da wannan kudirin, jim kadan bayan ganawar da suka yi a kusa da birnin London na Birtaniyan. Gwamnatocin kasashen biyu da wasu daga cikin ministocinsu za su rika tuntuba da kuma samun bayanai tsakaninsu sau guda a shekara, matakin da zai ba su damar tsara kawance ko kuma hadin kai a tsakaninsu. Merkel ta yi wa Johnson alkawarin cewa, ba da jimawa ba Jamus din za ta rage tsauraran matakan kariya da ta sanya kan kasarsa sakamkon nau'in annobar coronavirus na Delta da ake fama da ita a Birtaniyan.