Jamus da Faransa na fatan a rage ɗumamar yanayi
May 19, 2015Talla
Shugabanin ƙasashen Faransa da Jamus wato Francois Hollande da Angela Merkel da ke halartar wani taro kan canjin yanayi a Berlin,sun yi kiran da a cimma wata yarjejeniya wacce ka iya taimaka wa a rage ɗumamar yanyin da ake samu a duniya.
A sakamakon hayaƙin iskan guba da kamfanoni da masana'antu suka kan fitarwa galibi a ciki ƙasashe masu arziki.Taron wanda ke samun halartar wakilai daga ƙasashen duniya kusan 35 na ƙoƙarin samun daidaituwar baƙi a kan batun,gabannin taron Majalisar Ɗinkin Ɗuniya a kan ɗumamayar yanayi da za a yi a birnin Paris nan gaba a cikin watan Disamba da ke tafe.