Jamus da Faransa sun ja hankalin Rasha
December 28, 2018Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, sun bukaci Rasha da ta saki wasu jiragen ruwan nan na kasar Ukraine da ke a hannunta.
Cikin watan jiya ne dai Rasha ta kame jiragen na Ukraine a tekun Bahar Asuwad da ke yankin Kerch.
Hukumomin birnin Mosko dai sun zargi jiragen ruwan Ukraine 24 ne da shiga huruminsu ba tare da izini ba, sai dai Ukraine ta ce karfi ne kawai Rasha ke nunawa.
Angela Merkel da Emmanuel Macron, sun bukaci a sakar wa ma'aikatan jirage mara a yankin na Kerch.
Haka nan ma shugabannin biyu sun ce Rasha ta gaggauta sakin ma'aikatan jiragen na Ukraine da ke hannunta ba tare da wani sharadin ba saboda ba su damar bukuwan karshe da ma sabuwar shekara kamar kowa.