"Madame Stark" und "Monsieur Schwach"
May 30, 2013Kasahen Faransa da Jamus sun dauri aniyar gama karfi domin ceto nahiyar Turai daga matsalolin kariyar tattalin arziki da ta ke fama da su.A game da haka ne,a wannan Alhamsi Shugabar Gwamnatin Jamus Angela ta ziyarci birnin Paris, inda ta tattana da shugaba Fransois Hollande.Kasashen Jamus da Faransa na matsayin Hasane da Husaini a tafiyar da harkokin Kungiyar Tarayya Turai.Kasashen biyu wanda su ka fi karfin tattalin arziki daga cikin sauran kasashe membobin EU, suna taka muhimmiyar rawa cikin harkokin zarstawa na wannan kungiya.Babban burin da taron ya sa gaba shi ne, bullo da wani tsari na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, wanda za su gabatar a taron koli na shugabanin kasashe da na gwamnatocin Tarayya Turai da za a shirya wa ranekun 27 da 28 ga wata mai kamawa.
A yayin da take jawabi jim kadan kamin ta tashi zuwa birnin Paris, Angela Merkel ta baiyawa wajibcin gama karfi domin cimma burin da aka sa gaba:
Ta ce:Ya zama wajibi mu hada kai, mu gudu tare mu tsira tare, domin matsalolin tattatalin arzikin da kasashenmu ke fuskanta yanzu na bukatar cude-ni-in-cude ka ta gaskiya.Ta haka ne kawai za mu cimma buri bisa manufa.
Sai dai game wannan yunkuri na hada kai tsakanin Jamus da Faransa,shugaba Fransois Hollande na shan suka daga 'yan adawa, wanda ke suffanta shi da dan amshin shatan shugabar Gwamnatin Jamus.A cikin wannan wata ita kanta jam'iyya mai mulkin Faransa wato PS, ta yi huruci inda ta yi hannunka mai sanda ga Merkel ta rage shiga sharo ba shanu game da harkokin cikin gida na kasashen EU.
To saidai duk da wannan sabani da ake samu tsakanin Jamus da Faransa, kasashen biyu na matsayin kashin bayan EU inji Thierry Repentin, ministan kula da huldodi da kasashen Turai na Faransa, wanda kuma ya maida martani game da zargin da 'yan adawa ke wa Fransois Hollande na zama dan amshin shatan Merkel:
Ya ce: Mu san da cewar ba mu da akidodi iri guda tare da Jamus, amma duk da haka, muna zama teburin shawara mu cimma masalaha game da batutuwan da suka jibacin ci-gaban kasashenmu.Idan mu ka dauki misali da harajin da ake biya ga shigi da ficen kudade tsakanin wannan kasa zuwa wacen, Hollande ne ya kaddamar da shi ba Merkel ba, amma Jamus ta yi na'am da shi.Ta kamata mutane su daina tunanin cewar Jamus ce ke cilastawa sauran kasashen EU gudanar da tsare-tsarensu.
A sharhunan da suka wallafa jajibirin ganawar tsakanin tawagogin Jamus da na Faransa, kafofin sadarwa na kasashen biyu, sun kyautata zaton kara samun fahintar juna tsakanin bangarorin biyu.To sai dai ayoyin tambayar da su ka ta yi su ne wane tasiri tsarin na Merkel da Hollande zai yi wajen magance matsalolin da EU ke fuskanta.Sannan baki daya sun yi na'am da cewar, ma'amala tsakanin Faransa da Jamus a zamanin Fransois Hollande ta fuskanci koma baya, idan aka kwatanta da zamanin Nikolas Sarkozy.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohammad Abubakar